LABARAI

Wannan shine Me Lee, wadda yafi kowa kai ƙara a duniya, ya kai ƙarar taki kusan 3000

Wannan shi ne Mr. Jonathan Lee, mutumin da ya fi kowa kai kara a duniya.

– Jonathan har mahaifiyarsa ya shigar da kara a Kotu, inda ya fada ma kotu cewa mahaifiyar ta sa ba ta ba shi kulawa yadda ya kamata ba, a karshe dai Mr. Jonathan ya samu nasara a kan mahaifiyarsa inda ta biya shi $20, 000.

– Bayan wannan nasara ce Mr. Jonathan ya shigar da amininsa, da makocinsa, da wa su daga cikin yan uwansa, da budurwarsa, da yan sanda, sannan ya shigar da karar wani alkali, da wani kamfani, karshe har tsohon shugaban Amuruka George Bush ya shigar kara kuma duk ya sami nasara, a takaice dai ya shigar da kara sau dubu biyu da dari shida (2600).

– Daga baya aka sanya sunan Mr. Jonathan Lee, a matsayin wanda ya fi kowa shigar da kara a littafin tarihin nan na (World Guinness Book Record), ganin sunansa a cikin wannan tarihi Mr.

– Jonathan ya shigar da karar (Guinness Book of Record) gaban kotu bisa rubuta rayuwar sa a cikin littafin ba tare da amincewar sa ba, kuma ya samu nasara da kudi har $8, 000, 000.

-Bayan samun wannan nasara ne wani gidan talabijin ya nemi Mr. Jonathan, domin tattaunawa ta musamman, yayin tattaunar da suka tambaye shi ko mai ya sa yake rayuwa shi kadai ba shi da masoyi ko daya? Nan ta ke Mr. Jonathan ya fara dariya ya mike tsaye ya fice, ya yiwa kotu tsinke inda ya shigar da karar gidan Talabijin din bisa cin mutuncinsa a kan yimasa tambayoyin da suka shafi rayuwar sa domin tozarta shi, inda kotu ta ci tarar gidan Talabijin din $50, 000.

Me zaku iya cewa game da shi??

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker